Sarkin Kano Ya Yi Kira A Kwantar Da Hankali Yayin Jiran Kammala Zabuka

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II (Hagu) Ya Na Mika Kyauta Ga Muhammed Babangida, Wanda Ya Lashe Wasan Dawakai a Karakashin Kungiyar MTN a Lokacin Gasar Lashe Kofin Hassan E. Hadeja a Kaduna a Ranar 4 ga Watan Nuwamba, 2015

Kasa da sa’o’I 24 da sanarwa da hukumar zabe ta kasa a Kano ta bayar cewa, zaben gwamnan jihar bai kammalu ba, mai martaba sarkin Kano malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ja hankalin al’umar jihar su kwantar da hankali tare da zama lafiya da juna

A ganawa da manema labarai a fadar sa Sarkin na Kano ya ankarar da jama’a game da hurumin hukumar zabe ta kasa dangane da lamuran da suka shafi bayyana sakamakon zabe.

Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya yaba da rawar da Jami’an tsaro suka taka wajen tabbatar da cewa, zaben ya gudana cikin yanayi na lumana.

Sarkin na Kano ya yi kira da babbar murya ga talakawan Kano game da ni’mimin da ya yiwa kanawa da najeriya baki daya.

Yanzu haka dai al’amura su na ci gaba da dai-daita a birni da kewayan Kano bayan shafe kimanin kwanaki uku al’umar jihar na zaman dar yayin da ake dakon sakamakon zaben daya gudana ranar asabar.

A wani al’amari kuma, wasu ‘yan bindiga sun sace wani Engineer fara fata wadda ake zaton dan kasar Labanon ne yayin da suka kashe direban sa nan take a yau da safe.

Mutumin da aka sace din dai yana aiki ne da wani kamfani dake aikin gadar kasa dake shatale-talen Dangi na mahadar titin gida Zoo a nan Kano.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kano ya yi tsokaci kan zabe-4:04"