Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko Ya Rasu

Marigayi Sarkin Kagara, Mai Martaba Alhaji Salihu Tanko.

Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rasuwar Sarkin Kagara mai daraja ta daya mai martaba Alhaji Salihu Tanko da yammacin ranar Talata.

A wata sanarwa daga ofishin sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Ahmed Ibrahim Matane ta nuna cewa sarkin ya rasu ne a birnin Minna a sakamakon fama da rashin lafiya,

Barrista Abdulmalik Sarkin Daji kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Nejan ya ce rasuwar babban rashi ne bisa la’akkari da yadda Sarkin yake bayar da gagarumar gudummuwa wajen ci gaban al’umma kuma yana daya daga cikin sarakuna da suka fi dadewa.

Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar Nejan wanda dan asalin masarautar ne Alhaji Ibrahim Balarabe yace suna cikin juyayi matuka na wannan babban rashi na basarake mai hakuri da jama’arsa.

Garkuwan kagara Alhaji Yaro Namadi ya bayyana cewa suna cikin alhini na rashin shugaba mai kaunar jama’a da tausayin yara.

Margayi Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko ya rasu yana da shekaru 102 kuma ya hau kan karagar mulki ne a shekarar 1981, kenan ya share kimanin shekaru 35 akan karagar mulki, ya rasu yabar mata 2 da yara 15 da kuma jikoki da dama, tini dai akayi jana’izarsa a fadar sarkin dake garin Kagara.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

Your browser doesn’t support HTML5

Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko Ya Rasu


Karin bayani akan: jihar Nejan, Sarkin Kagara Alhaji Salihu Tanko, Nigeria, da Najeriya.