Yayin da suka kaimas gaisuwar sallah sarakunan Adamaw sun gana da gwamnansu dangane halin da jiharsu ta samu kanta
WASHINGTON, DC —
Yayin da sarakunan gargajiya na jihar Adamawa suka kai ma gwamnansu gaisuwar sallah sun dauki lokaci sun tabo matsalolin da suka addabi jihar.
Kama daga dokar ta baci da ambaliyar ruwa da ma rikicin siyasa su ne suka addabi jihar Adamawa da suka sa duk wani aikin cigaba ya tsaya. Wadannan matsalolin suka sa sarakunan da suka kaima gwamnan gaisuwar sallah suka tabo batutuwan. Lamidon Adamawa shugaban majalisar sarakunan jihar Dr. Barkindo Aliyu Mustapha ya ce muddin 'yan siyasar jihar basu kai zuciyarsu nesa ba to ko da wuya a samu cigaba a jihar. Shi kuma gwamnan ya yi kwatanta rikicin siyasar jihar da wata rina dake neman doki. Ya kuma ce rashin aikin yi na matsa da kuma rike kudin jihar da gwamnatin tarayya ta yi su ne suka kara haddasa matsalolin jihar. Kudaden da gwamnati tarayya ta rike sun kusa biliyan casa'in. Don haka ya roki jama'ar jihar da suka kara hakuri da tafiyar hawainiya da jihar ke yi.
Gwamnatin Adamawa tana bukatar a biyata kudaden da ta kashe kan hanyoyin gwamnatin tarayya dake jihar kafin tafiya ta yi tsami tsakanin gwamnan da wasu 'yan siyasar jihar dake Abuja.
Wasu 'yan jihar sun roki 'yan siyasar jihar da su yi hakuri su dubi talakawan jihar domin su ne ke ji a jikinsu. Sun ce talakawa ne ke cikin halin kuncin wahala domin dambarwar siyasar jihar. Sun rokesu su daidaita ko jihar ta samu zaman lafiya da cigaba.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5