Sanusi Lamido Zai Kalubalanci Dakatarda Shi a Gaban Kotu

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi.

Gwamnan babban bankin Najeriyan wanda yake ziyarar aiki a Nijar, yace bashi da wata nadama.
Malam Sanusi Lamido Sanusi wanda ya sami labarin umarnin dakatar da shi da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayar da safiyar yau Alhamis yayinda yake ziyarar aiki a Nijar ya gayawa manema labarai a tashar saukar jiragen sama dake Niamey cewa ba zai koma bakin aiki ba, amma zai dauki matakin shari'a domin tantance ko shugaban kasa yana da hurumin dakatar da gwamnan babban bankin.

Mallam Sanusi yace "da farko dai Alhamdulillahi, kuma dama wannan aiki dai munzo karshensa, kuma duk wanda ya sanni ya san cewa da son raina ne da tuni na tafi sabo sanin yadda muke takun saka da gwamnati karshenta ba za a rabu lafiya ba."

Mallam Sanusi ya kara da cewa "babban abunda zan fada shine na godewa Allah da Ya bani iko na bautawa kasa, kuma na gode Masa da ya bani karfin zuciyarda na yi abubuawa da na yi.

Ga cikakkiyar maganar da Mallam Sanusi yayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Sanusi Lamido Zai Kalubalanci Dakatarda Shi a Gaban Kotu - 1:49