O'Connor, wacce ta yi ritaya a shekara ta 2006, ta mutu a jiharta ta Arizona sakamakon ciwon mantuwa na kwakwalwa da kuma cutur numfashi.
Babban mai shari'a John Roberts ya fada a cikin wata sanarwa cewa O'Connor "ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko a kasarmu da ta zama alkali."
O'Connor ta girma ne a kan Lazy B, wani wurin kiwon shanu mai fadin eka 160,000 a cikin babban yankin hamada da ke kan iyakar Arizona da New Mexico.
Bayan shekaru hudu tana aiki a ofishin babban lauyan jihar Arizona, an nada ta don cike gurbin kujerar Majalisar Dattawan jihar a shekarar 1969. Bayan da aka sake zaben ta, sai ta zama mace ta farko a kasar da ta zama shugabar masu rinjaye na Majalisar Dattawan jihar.
A cikin 1981, a yayin da Shugaba Ronald Reagan ke neman wanda zai taimake shi ya cika alkawarin yakin neman zabe na nada mace a Kotun Koli, ya samu shawarwari game da ita masu mahimmaci. Lamarin da ya yi sandiyar cika wannan alkawarin. Ta yi kama da mai ra'ayin mazan jiya a yayin zamanta na tabbatar da Majalisar Dattawa, inda ta nuna adawa da ra'ayin cewa 'yancin zubar da ciki ya cancanci karewa a tsarin mulki.
"Ra'ayina a fannin zubar da ciki shine ina adawa da hakan a matsayin batun hana haihuwa ko akasin haka," in ji ta.
Nadin O'Connor a matsayin mace alkali ta farko mai adalci ba kawai ya kafa tarihi ba ne, ya kuma zaburar da wasu jihohi su fara sanya mata a kotun koli.
O'Connor ta bar 'ya'ya uku da jikoki shida. Mijinta ya rasu a shekara ta 2009.