Shugaban majalisar Dr Bukola Saraki na fuskantar tuhuma a kotun kula da da'ar ma'aikata dangane da rashin bayyana kaddarorinsa yayinda ya tsaya takarar neman gwamnan jihar Kwara shekaru goma sha uku da suka wuce.
Sanata Ibrahim Gobir daga jihar Sokoto yana cikin wadanda suka raka Dr Saraki kotu a zamanta na biyu. Yace ba wani abu ba ne kokari ake yi a jawo masa matsala. Batutuwan da suka kawo suna da ban dariya. Yace yaushe cin bashi ya zama haram? Ana dai son a cutar da shi ne.
Batun tsige Saraki daga mukaminsa abu ne mai kaman wuya domin sai an samu amincewar biyu bisa uku na 'yan majalisar. Babu tabbacin samun hakan
Sanata Isa Hamma Misau yace basu da wannan hadin kan domin jam'iyyar bata da gaskiya. Bata yiwa Saraki adalci. Suna nuna masa kiyayya. Me ya sa basu sa Faleke gaba ba wanda yaki ya je ya zama mataimakin gwamnan jihar Kogi. Ya fito kafar talibijan ya yi kacakaca da shugabancin jam'iyyar kuma basu yi masa komi ba. Basu sa Faleke gaba ba domin yana da ubangida ba kamar Saraki ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5