Da yake mayar da martani ga tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Haruna Dauda yayi masa, Sanatan ya bayyana cewa bayan nasarar da aka samu a yakunan, sabon yakin dake gaba shine yadda za’a magance yunwa da talauci da rashin abinci musamman tsakanin yara kanana.
Ya ce wannan ba yaki ne da ya shafi gwamnati kadai ba, yaki ne da ya shafi alumma gaba daya domin a cewar sa, shekaru uku Kenan rabon jama’a da zuwa gonakin su, dan haka ya kamata jama’ su sa hannu domin taimakawa juna da kuma wadanda suka sami kawunansu cikin wannan hali.
Sanata Ndume ya bayyana cewa talauci ba sabon abu bane amma yunwa daban take da talauci, domin kuwa idan kana da kadan, daban yake da babu gaba daya, domin akwai jama’a da dama da basuda komi a sakamakon rashin samun damar zuwa gonakin su.
Da yake ci gaba da amsa tambayoyin, sanatan ya bayyana cewa sun je jihar Borno ne domin rabar da abincin da shugaban kasa yasa a ba talakawan jihar ne, amma a cewar sa abincin da suka taras bai ki adadin wanda shugaban kasa ya aiko da shi ba. Domin a cewarsa tireloli dari da goma sha uku, amma da aka zo wurin da za’a rabar da abincin sai suka ga bai kai yadda ya kamata ba, tireloli hansin da uku kacal suka rage.
Ta dalilin haka ne Sanatan ya ce ya dakatar da rabon abincin domin daukar matakin da ya dace, ya kara da cewa ana kyautata zaton cewa hukumar EFCC ta cafke dan kwangilar domin tuhumar sa.
Ga cikakkiyar hirarsu da Haruna Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5