Tsohon shugaban gwamnan Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Muhammad Makarfi ya bayyana aniyarsa ta neman jam’iyar su ta PDP ta tsayar da shi dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.
Sanatan yace, bayan ya kammala zagayen tuntuba, shi ma ya yanke shawarar shiga takarar wanda ya kawo adadin wadanda suke neman kujerar shugaban kasa daga arewacin Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP zuwa hudu.
Yayinda yake tattaunawa da sashen Hausa Sanata Makarfi ya nuna damuwa da yadda tsaro ya tabarbare a kasar. Y ace “wasu da suka fito daga Birnin Gwari suna cewa masu garkuwa da mutane sun saki mutanen da suke rike dasu domin su tafi yin sallah amma sun yi kashedin cewa da zara an gama bikin sallah kowa ya shiga taitayinshi”
Abun da masu satar mutanen suka yi tamkar nuna babu gwamnati ke nan a kasar a cewarsa. Yace maganar tsaro ba ta siyasa ba ce. Magana ce da ta shafi kowa da kowa.
Yace gwamnati na batun Boko Haram, inda a gaskiya ta samu nasara amma bata kawo karshen ta’addancin ‘yan kungiyar ba. Ya yi kira ga gwamnatocin jihohin da lamarin ya shafa da su hada kai ga gwamnatin tarayya domin ta kawo karshen aika aikar gaba daya.
Sanata Makarfi ya bayyana bukatar a zakulo bata gari dake hada baki da muggan mutane suna aiwatar da ta’addanci.. Dole a yi fatali dasu.
Da ya juya kan masu aikin tsaron sai y ace idan shi ne zai fada masu abun da yake so ya basu duk akayan aikin da suke bukata da kudaden amma idan suka kasa to su kuka da kansu.
Akan tuntubar da ya dade yana yi a duk fadin kasar bincikensa ya nuna “zai yi kyau idan zan shiga jerin gwanon sauran ‘yan jam’iyyarmu da suka nuna sha’awa a neman yaddan Allah da na jama’a a tsayar dasu ‘yan takara”. Nan ba da dadewa ba Sanata Makarfi zai kaddamar da neman zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa ta PDP.
A saurari rahoton Isah Lawal Ikara da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5