Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar sun nuna cewa an samu saukar farashin kayayyaki a kasuwanni cikin makwannin nan, kuma hakan bai rasa nasaba da matakan da ake dauka. Gwamnatin Nigeria ta ce akwai fatan cewa, tattalin arzikin kasar zai farfado nan da karshen wannan shekara.
Domin jin yadda ‘yan kasuwa da masu sayan kayayyaki ke gani game da wannan ci gaba da hukumar kididdigan tace an samu ayanzu, wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, ya leka jan Block ‘daya daga cikin manyan kasuwanni a jihar Adamawa.
Dayawa daga cikin mutanen da Abudul’aziz ya zanta da su a kasuwar, sun nuna cewa babu wani sauyi da suka gani akan farashin kayayyaki.
Shugaban kungiyar Rana ta fito, ‘daya daga cikin manyan kungiyoyin ‘yan kasuwa a Najeriya, Alhaji Kawule Dasin, yace su basu tabbatar da wannan rahoto na hukumar kididdigan ba.
Najeria, wadda ke cikin jerin kasashen da ke kan gaba wajen albarkatun Man Fetur a nahiyar Afirka, ta dogara ne kacokan bisa kudaden da ake samu daga Man. Kuma wasu na ganin faduwar farashin man ne a kasuwar duniya ta haddasa wa kasar halin da take ciki a yanzu, koda yake wasu masu fashin baki na ganin cewa irin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka ne suka kara janyo tabarbarewar al'amuran batun da jami’an gwamnatin kasar ke musanatawa.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5