An sami sabani tsakanin bangarorin biyu lokacin da wasu mutane biyu 'yan gida daya suka Shiga takarar kujerar hakimin Jada kuma ko wannensu da bangaren da ke goya masa baya.
Amma ana tsammanin lafawar kura bayan nadin sabon hakimin Jada Alhaji Umar Ardo sai gashi daya daga cikin masu yiwa tsohon shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, wato Alhaji Mohammed Suleiman Baba Jada ya je kotu inda ya yanki takardar daukar rantsuwa ranar ashirin da shida ta watan Afrilu shekarar nan don gabatar da shaida ga hukumomin tsaro yana zargin Walin Ganye Alhaji Sadiq Kalu da kungiyar kwankwasiya da niyyar tada zaune tsaye ta hanyar harzuka matasan yankin.
Amma Walin Ganye ya musanta zargin. Ya martanin cewa ba shi da wata alaka da kungiyar ta kwankwasiya. Ya hada da cewa kamata ya yi dattawa kaman su Alhaji Mohammed Suleiman Baba Jada su nemi hanyoyin dinke baraka lokacin da aka sami sabanin ra'ayi maimakon kalan maganganu.
Wani mazaunin garin Jada Malam Yahya Dan Maisamari ya tabbatarwa sashin Hausa takarar kujerar hakimin ce ta yi sanadiyyar raba al'ummar musamman matasan Jada gida biyu lamarin da ke da hatsari ga zaman lafiyar yankin.
Ga Karin bayanin daga rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum