Samsung Zata Fitar Da Sabuwar Wayar Hannu Galaxy Note 8

Samsung Note

Kamfanin Samsung na shirin fitar da sabuwar waya cikin jerin wayoyinsa na Galaxy Note, wadda ya kayata da fasahar zamani dake dauke da babban allo da tsinken rubutu da kuma kamarar daukan hoto mai kyawun gaske.

Lokaci ya yi da ake sa ran Samsung zai fitar da bayanan wayar Galaxy Note 8, a wani babban taron manema labarai da za a gudanar gobe Laraba, 23 ga watan Agusta idan Allah ya kaimu.

Wayar Galaxy Note ta baya-bayan nan da Samsung ya fitar na ‘daya daga cikin manyan wayoyin zamani da mutum ka iya mallaka. Amma wayar ta samu matsala, bayan fitowar rahotanni masu yawa na cewa batirin wayar na ‘daukar zafi, wanda hakan ya tilastawa kamfanin kiranyen duk wayoyin da ya sayar a fadin duniya.

Samsung ya sake samun karbuwa ga mutane bayan da ya fitar da wayarsa ta Galaxy S8, wadda ta zamanto ‘daya daga cikin manyan wayoyin Android da ake da su a wannan shekara. Amma Samsung na fatan sabuwar wayar Note 8 za ta sake dawo da martabar kamfanin.

Your browser doesn’t support HTML5

Samsung Zata Fitar Da Sabuwar Wayar Hannu Galaxy Note 8 - 1'11"