Kamfanin Samsung ya bada sanarwar yiwuwar zarce kanfanin Apple wajan ingancin fasaha a yayin da yake shirin fitar da wata sabuwar wayarsa mai murfi wato wadda ake nunkewa.
Daya daga cikin manyan shugabannin kanfanin Mr. DJ Koh, mai kula da harkokin wayar hannu a kafar talabijin ta NBC, a ranar litini ya bayyana cewa kanfanin ka iya fito da sabuwar waya irin wadda ake nunkewa a babban taron kanfanin da za a gudanar cikin watan Satumba, yayin da ake sa ran shi ma kanfanin Apple zai fito da tasa.
Ku Duba Wannan Ma Samsung Galaxy Note 9 Ta BayyanaShugaban bai bayyana takamaimai lokacin da wannan sabuwar waya zata shiga kasuwannin ba, koda shike a wani lokaci ya taba bayyana kaddamar da wayar cikin wannan shekarar kokuma mai zuwa.
Ana kyautata zaton idan kanfanin ya fito da wayar wadda y ace mai saukin farashi, zata iya sauya tunanin jama’a da dama dake amfani da wayar Apple.
Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da wannan waya da akai wa lakabi da Galaxy X. Amma ana kyautata zaton girmanta zai iya kaiwa kamar na dan karamin Tablet, wato girmanta zai iya na waya kadan sannan mai amfani da ita zai iya nunke ta, ya kuma bude lokacin da yake bukatar amfani da ita.