Sama Da Mutane Dubu 10 Sun Tsere Daga Garin Baga Zuwa Maiduguri

Yan Gudun Hijirar Baga

Yan gudun hijira daga garin Baga sun koka da irin halin da suke ciki, tun lokacin da suka tsere daga garuruwan su zuwa Manguno da babban birnin jihar Borno, Maiduguri. saboda yadda 'yan Boko Haram su ke kona gine-ginan gwamnati dana manyan mutane a garin.

Hukumar samar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno wato SEMA ta ce akwai a kalla mutane sama da dubu goma da suka tsere daga garuruwansu, sakamakon rikicin mayakan Boko Haram, zuwa garuruwan Manguno da babban birni jihar Maiduguri da kuma wasu kauyukan da suke kusa don neman samun mafaka.

Shugabar Hukumar samar da Agajin Gaggawa ta jihar Borno Hajiya Ya Bawa Kolo ta shedawa Sashen Hausa cewa, sun samar da kayayyakin abinci ga wadannan mutane da rikicin Boko Haram ya daidaita, wanda ta ce yanzu haka sun shigo da tirololin abinci da kayayyakin masarufi har guda talatin, don tallafawa wannan mutane da suka gujewa wannan rikici.

Kolo ta kara da cewa, yanzu haka suna kokarin samarwa da ‘yan gudun hijirar gurun da zasu zauna, wanda mafi yawansu sun fitone daga garuruwan Baga kuros da Doron Baga dake karamar hukumar Kukawa, sune rikicin y araba da gidajensu.

Wasu da suka gujewa rikicin sun fadawa Sashen Hausa cewa, mayakan Boko Haram ne suka sa suka fice daga garuruwansu, inda suka shafe kwana biyu suna tafiya a kafa daga garin Baga zuwa Manguno, babu abinci sai dai ruwa kawai suke sha har suka isa garin Manguno. Sun yi kira da gwamnatin data sama musu gurin kwana da bandaki, saboda yanzu a waje suke kwana ga sanyi ga iska yana damun su. Sannan sun ce yanzu haka babu soja ko daya a garin na Baga.

Amma Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan Najeriya Birgediya Sani Usman Kuka Sheka, ya karyata wannan batu cewa, ‘yan Boko Haram ne suke rike da garin na Baga.

Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda Biu

Your browser doesn’t support HTML5

Sama Da Mutane 10,000 Sun Tsere Daga Garin Baga Zuwa Maiduguri