Sakonni Ga Matasa Domin Kauracewa Harkar Dabar Siyasa - Jackzy

Adamcy Maina Janko

Adamcy Maina Janko, wanda aka fi sani da Mr Jackzy – ya kan isar da sakonni ga matasa musamman ga dabi’ar nan da ke ciwa matasa tuwo a kwarya ta matsalar shaye-shaye da ake fuskanta a yanzu take kuma tauye masu cigaban rayuwa.

Ya ce ko da ma can asalin wakar hip-hop da ta fito daga kasar turawa ana yin ta ne domin nuna irin batanci, da banbancin launin fata da ake yi wa bakake a kasashen turawa, wanda shine su ma mawakan hip-hop ke daukar salon don fadakarwa a tasu nahiyar a yanzu.

Ya kara da cewa wakarsa ta fi maida hankali ne ga matsalolin matasa a yanzu da ma wasu hanyoyin magance su, Jackzy ya ce wakar sa ta gaba zata maida hankali ne ga jan hankali don kauracewa bangar siyasa ko harkar daba, musamman ma a yanzu da aka kusa shigowa kakar siyasa da zabe.

Daga karshe Jackzy, ya ce ya fuskanci kalubale da dama da ya fara harka ta waka, wajen samun damar daukar nauyin fitar da wakarsa a lokacin da ya fara hakan ce ma ta sa a yanzu ya bude studio domin tallafawa kananan mawaka da ke tasowa.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Zasu Iya Amfani Da Basirar Da Allah Ya Basu Wajen Kawo 3' 10"