Sakon Buhari Akan Azumi

[FILE PHOTO]

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan Najeriya akan suyi addu’o’in samun zaman lafiya, da cigaba a kasar baki daya a dai-dai wannan lokaci da Musulmai ke fara azumin watan Ramadan na shekara ta 2015.

A wani sakon taya murna da shugaban ya fitar da bakin kakakinsa Mallam Garba Shehu, Buhari yayi kira ga Musulmai akan su nemi amfanin wannan wata ta taimakawa sauran jama’a, da koyon darrusa da kuma bin sakonnin da addini ya tanada kamar yadda Manzon Allah ya koyar.

Shugaban a sakon shi yayi kira kai tsaye ga masu tayar da tarzoma da sunnan addinin Musulunci akan su dena bata wa addinin suna.

Buhari yace “a dai-dai wannan lokaci da muke kokarin kawo masalaha na dun-dun ga rigingimun Boko Haram a kasashen dake makwabataka da tabkin Chadi, bari nayi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan uwanmu wadanda suka kauce hanya akan su ajje makamansu, su rungumi zaman lafiya, sannan su nemi karin ilimin addinin Musulunci a wannan lokaci da ma sauran lokuta.”

Shugaban yayi addu’an samun zaman lafiya a duk bangarorin kasar da duniya baki daya.