Sako 'Yan Matan Chibok 21 Ya Zowa Mutane Bazata

Wasu iyayen 'yan matan Chibok

Sako 'yan matan Chibok 21 cikin 219 da kungiyar Boko Haram ta sace fiye da shekaru biyu da suka gabata ya zowa mutane bazata tare da rashin bayani akan yadda suka fito.

Labarin sakin 'yan matan su ishirin da daya ya zowa mutane da mamaki saboda babu takamaiman bayani daga hukumomin tsaron kasar Najeriya.

Ba'a sani ba ko sojoji ne suka kubutar dasu ko kuma jami'an DSS ne suka yi aikin bayan sun musanyasu da wasu 'yan kungiyar Boko Haram dake hannun su DSS din. Ko can bayan ita kungiyar tayi tayin yin musayan 'yan matan da sako 'yan kungiyarsu.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fannin labarai Garba Shehu ya fitar da wata sanarwa inda ya tabbatar da sako wasu daga cikin 'yan matan. Ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa ne zai karbi 'yan matan.

Ita ma gwamnatin Borno tace har yanzu bata samu wani bayani daga hukumomin tsaron kasar ba game da sakin 'yan matan kamar yadda mataimakin gwamnan Alhaji Hassan Durku ya shaida. Yace yadda 'yan jarida suka ji haka shi ma ya ji. Suna dkon jami'an tsaro su yi masu bayani akan lamarin.

Wasu 'yan jihar Borno da aka tuntuba akan wannan labari sun nuna farin cikinsu idan har hakan ya faru.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sako 'Yan Matan Chibok 21 Ya Zowa Mutane Bazata - 4' 07"