'Yan bindiga na ci gaba da hana jama'a bacci da ido biyu a rufe a wasu sassan Najeriya, duk matakan da mahukuntan kasar su ke cewa suna dauka.
Yankin Goronyo yana a gabascin Sakkwato, yankin ne da ya jima yana fama da matsalolin 'yan bindiga.
A kwananan ma 'yan bindigar sun hallaka mutane da dama a garuruwan Giyawa, Sabon Garin Dole, Boye Kai da sauran garuruwan Goronyo, abin da ya harzuka matasan yankunan suka soma matakan kare garuruwan su daga barazanar 'yan bindigar.
Kantoman karamar ta Goronyo Kabiru Shehu ya tabbatar da cewa tura ta fara kaiwa bango ga yadda 'yan bindigar ke addabar jama'ar yankunan.
Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu Sakkwato a wata ziyayrar ja je da ya kai wa jama'ar yankunan akan ta'addacin da suke fuskanta yace suna daukar matakai na magance matsalolin.
Yayin da jama'ar Goronyo suka soma yin kukan kura suka tunkari, 'yan bindiga, su kuwa jama'ar Wurno, duk a gabashin Sakkwato, a iya cewa tsugune ba ta kare ba, domin bayan hare-haren da aka kai garuruwan su a kwanakin baya, a ranar Lahadin wannan mako sun karbi bakuncin wasu 'yan bindiga.
Shehu Abubakar Barayar Zaki daya ne daga cikin mutane biyar da ke karbar magani a asibiti, sanadiyar harbin da 'yan bindiga suka yi musu, lokacin da mutane hudu suka riga mu gidan gaskiya.
Kantoman karamar hukumar ta Wurno Kabiru Hali yace tuni anyi jana'izar mutanen hudu.
Duk wadannan matsalolin suna faruwa ne lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatocin jihohi ke cewa suna daukar matakan magance ayukkan 'yan bindigar duk da yake har yanzu jama'a na cewa basu gani a kasa ba.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5