Sakina Rabiu Muktar – matashiya mai sana’ar sayar da atamfofi da mayafai da sauran kayan kyalkyali na mata, ta ce lokaci ya wuce da mace zata tsaya tambayar saurayinta ko mai gidanta idan tana da aure kudaden kashewa.
Ta ce 'yan mata a yanzu suna jajircewa su kuma kauracewa yawan bani-bani, domin tsira da mutuncinsu, inda ta ce ta fara ne da karbar kayan wasu ta sayar musu, ta sami riba har ta kai ta da samun jarin ta na kanta.
Kuma mafi yawan sana’o'inta tana yi ne ta hanyar amfani da shafin sadarwa na zamani, wajen tallata hajjarta, sannan sai an tura mata kudi ne sannan take tura kayanta sakamakon rashin yarda da ake fama da ita.
Tana mai jan hankalin mata da su kauracewa bin samari wajen aikata aikin abinda bai dace ba domin karbar kudi a wajen su.
Daga cikin kalubalen da Sakina ta fuskanta a shekaru biyar da fara sana’ar hannu, ta ce shine wata matsala da ta shiga sakamakon baiwa mata kaya na kimanin dubu dari uku, a wajen hada lefe wanda ta gudu da kudadenta.
A yanzu malama Sakina ta ce ta daina bada kaya bashi, idan kuwa 'yan karba da biya na karshen wata ne sai an yi yarjejeniya a rubuce kafin ta bayar.
Daga karshe ta ce tana hada makarantar gaba da sakandire, a lokaci guda kuwa ta harkar kasuwanci ta.
Your browser doesn’t support HTML5