Sakataren Tsaro Amurka da Firayim Ministan Israila Sun Gana

Ash Carter sakataren tsaron Amurka da Firayim ministan Israila Benjamin Netanyahu

Ash Carter na Israila saboda ganawa da firayim ministan kasar Benjamin Netanyahu

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter zai gana da firayin ministan Isra’ila Bejamin Netanyahu yau Talata don tattaunawa, mako daya biyo bayan kulla yarjejeniyar shirin makaman nukiliyar Iran wadda Mr Netanyahu din ke adawa da ita.

Mr. Carter ya nemi ya karfafa guywar Isra’ila jiya litinin, inda ya kira kasar tushen da Amurka ke amfani da ita wajen yin dabarunta a gabas ta tsakiya.

Mr. Netanyahu ya soki shawarwarin yarjerjeniyar makaman nukuliyan tun da farkon fari har zuwa kulla ta a makon da ya wuce, bayan da Amurka, da Britaniya, da china, da Faransa, da Rasha da Jamus suka kulla yarjejeniyar da suka dade suna neman kullawa, mr. Netanyahuwa y kira ta a matsayin kuskure na tarihi.

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ba tare da wata cirjiya ba ya yarda da yarjejeniyar jiya litini, tare da kara janyo suka daga jakadan Isra’ila a MDD Ron Prosor, wanda “Ya kira wannan yarjejeniyar “bala’i”

Mr Prosor yace, yanzu Iran zata yi amfani da kudi dala biliyan 150 akan ‘yan kungiyoyin ta’adda. Amma tambayar da yayi it ace har nawa za a kashe akan Hezbollah da Hamas? Nawa za a kashe akan shugaban Syria Bashar al-Assad? Kuma nawa za a kashe akan ayyukan ta’addanci a fadin duniya.

Jakadiyar Amurka a Majalisa Dinkin Duniya Samantha Power ta yaba da kwamitin sulhun, akan gwajin diplomasiyya, inda ta kara da cewa yarjejeniyar ba za ta gusar da damuwar Amurka akan Iran ba. Ta kuma ce wannan damuwar ta kunshi take hakkokin bil’adama, da kuma goyon bayan ‘yan ta’adda da Iran ke yi da kuma shirin ta na makamai masu linzami.