A daya bangaren kuma, Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki moon, ya gana da shugaban kasar Gabon Ali Bongo ta wayar tarho da kuma abokin hamayyarsa Jean Ping, inda ya yi kira a garesu da su kawo karshen rikicin siyasar da ke faruwa a kasar.
WASHINGTON DC —
Zanga zanga dai ta barke a ranar Laraba, bayan da aka ayyana Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi da ‘yar tazara.
Sakamakon zaben ya nuna cewa Bongo ya samu kashi 49.8 na kuri’un da aka kada yayin da Ping kuma ya samu kashi 48.2.
Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Gabon, Pacome Moubelet, ya ce ya zuwa yanzu an cafke mutane sama da dubu daya a duk fadin kasar, ciki har da wasu 800 da aka kama a babban birnin kasar.
Ya kuma tabbatar da mutuwar mutane uku a tashin hankalin.
Sakatare Janar Ban ki moon, ya kuma nema a bar wakilinsa na tsakiyar Afrika, Abdoulaye Bathily, da ya ci gaba da aiki da bangarorin da ke takaddama da juna, domin a kawo karshen rikicin.