Da yake zantawa bayyanawa manema labarai matsayar da aka cimma a taron, gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce a tarihin tarukan da ake gudanarwa ba a taba gudanar da taron da gwamnoni suka halarta ba. Wanda aka tattauna kan matsalolin dake damun Arewa.
A taron an kafa kwamitoci har uku da ciki harda kwamitin da zai duba “sake gyara zama a Najeriya” ya kuma duba halin da ake ciki kan batun gyran tsarin mulki. Sai kuma batun rikicin Fulani da Manoma.
Taron ya yi Allah wadai da abin da ya faru ga mutanen da suka je neman Mai a tafkin Chadi, kuma an yanke hukuncin gwamnoni a kalla tara zasu je Borno don yin ta’aziyya da jaje.
Haka kuma taron ya tattauna kan rikici da ya faru a kauyen Kajuru na jihar Kaduna, inda aka yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan hukunta duk mutanen da ke da hannu a rikicin.
Domin karin bayani saurari bayanin gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari.
Your browser doesn’t support HTML5