Shugaba Rafael Correa, ya ce mutane 272 ne suka rasa rayukansu, kuma ana sa ran adadin zai karu sosai yayin da akalla mutane 2,500 suka samu raunuka.
A lokacin da bala’in ya auku, shugaba Correa na kasar Italiya, inda ya yi maza-maza ya datse ziyarar ta shi domin komawa gida ya shirya ayyukan kai dauki.
A lokacin da ya ke jawabi a Manta, wato daya daga cikin wuraren da girgizar kasar ta fi shafa, shugaban ya ce yanzu an fi maida hankali ne wajen neman wadanda suka tsira da ransu.
Ya kuma ce akwai alamu da ke nuna cewa akwai mutane makale a karkashin baraguzai.
Wannan girgizar kasa mai karfin maki 7.8, ita ce mafi muni da ta taba faruwa a kasar, tun bayan wacce aka gani a shekarar 1949 a yankin Ambato, wacce ta kashe dubban mutane.