Kamar yadda muka alkawarta wa mai sauraro zamu kawo muku sakamakon gasar Freedom radio Meko award da aka gabatar makon da ya gabata, a cikin wadanda suka lashe gasar su goma sha shida.
A jiya ne sakamakon gasar ya fito, inda a bangaren Nanaye da Soyayya wadanda suka lashe gasar dai mawaka hudu suka samu nasara, daga cikinsu akwai, Ibrahim Home Boy wanda shi ya zo na daya, sai Nazifi Kada sai kuma Zaks M Ibrahim wanda shi ne ya zo na hudu.
A bangaren Nanaye da Fadakarwa kuwa wannanfannin ma mawaka hudu ne suka lashe gasar, da suka hadar da Abdul D Jaen, sai Ahmad Sadiq Kurna da kuma Safyanu Sas da kuma Abubakar Sadiq.
Idan muka leka fannin Hip-hop soyayya kuwa akwai Usman Suleman wanda aka fi sani da Shamaki, Dj on Top da kuma sai Maza na karshen su kuwwa Sassafe.
A hip-hop fadakarwa kuwa wandanda suka lashe gasar sun hadar da mace kamar maza, Queen Zee shaq ce ta zo ta farko sai Free boy da kuma Yusuf Maza ne na karshensu kuma Mahmoud Musa.
Mun kuma samu zantawa da alkalan gasar dangane da yadda gasar ya wakana da kuma hanyoyin da suka bi wajen fitar da zakaru, inda Nazifi Asnanic ya tofa albarkacin bakinsa, ya ce yana cikin wadanda suka gudanar da alkalancin kasancewar shi ahalin abin ne kuma dole ne a jinjina wa gidan rediyon da ya shirya wannan gasar, a cewarsa hakan zai baiwa mawakan kwarin gwiwa wajen inganta wakokinsu, tare da fatan wadanda suka shiga gasar sun gamsu da alkalancin da a yadda aka fitar da zakarun.
Hussaini Danko shima cewa gasar abu ne mai kyau wanda zai karawa mawaka kwarin gwiwa
kamar yarda takwaransa yace duk abinda yake a bayyana yake yana da saukin alkalanci, inda yake cewa suna duba ma’anar waka a rubuce da irin sakonnin da wannan waka ta fitar kafin tantace wadanda suka lashe gasar’
An dai gudanar da wannan sakamakone a harabar gidan rediyo freedom a jiya lahadi, inda suka karbi lambar girmamawa tare da nuna farin cikinsu.
Your browser doesn’t support HTML5