Sakamakon Binciken Abin Da Ya Fi Kashe Matasa A Duniya

Hukumar lafiya ta duniya ta fitar da wani sakamakon bincike da ya shafi abin da ke kashe matasa a duniya.

Binciken ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne suke mutuwa kowacce shekara, kwatankwacin mutane dubu uku kowacce rana.

Bisa ga binciken, hatsarin mota shine kan gaba a jerin sanadin asarar rayuka, wadansu sanadin kuma sun hada da cutar dake hana lunfashi, da kuma kisan kai.

Rahoton ya nuna cewa, abinda yake yawan janyo asarar rayuka ya banbanta bisa ga jinsi, ko shekaru, ko addini. Bisa ga rahoton, samari ‘yan shekaru sha biyar zuwa sha bakwai sunfi fuskantar barazanar rasuwa ta hadarin ababan hawa fiye da ‘yanmata, ko kananan yara maza. A Afrika kuma, kananan yara sunfi fuskantar barazanar kamuwa da kwayar cutar HIV.

Yayinda ‘yammatan tsakanin shekaru goma zuwa goma sha hudu suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar hakarkari sabili da shakar hayakin murhu, yammatan tsakanin shekaru goma sha biyar zuwa sha tara kuma suke fuskantar barazanar mutuwa ta dalilin matsalolin da suka shafi daukar ciki, da haiuwa da kuma zubar da ciki ta hanyar dake da hatsari.