A karshen wani taron kwanaki biyu da aka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, kwamandojin rundunonin mayakan kasashen yankin tafkin Chadi sun jaddada aniyar kara jan damarar Yaki da nufin kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram nan ba da jimawa ba don ganin zaman lafiya ya tabbata.
Taron wanda ya hada kwamandojin rundunonin kasashe 5 Najeriya, Nijar, Chadi, Cameroun da jamhuriyar Benin, a daya gefe masu ruwa da tsaki a sha’anin tafiyarda ayyukan rundunar hadin gwiwar MNJTF ya fara da nazarin halin da ake ciki dangane da yakin da dakarun wadanan kasashe ke gudanarwa da kungiyar boko haram a kewayen tafkin Chad, kafin daga bisani a umurci mahalartan akan bukatar kara jan damara.
Ambasada Maman Nuhu shine sakataren zartarwar kungiyar kasashen CBLT. Da yake jawabin rufe taro kwamandan rundunar asakarawan Nijar Gen. Ahmed Mohamed ya bayyana cewa. Yakin da muke yi a yau abu ne da aka tilasta mana yinsa, domin an tsokano shi ne ba tare da wata kwakwarar hujja ba, to amma duk da haka ya zama dole mu dage donganin mun yi galaba.
Nayi nan bada dadewa ba za muyi nasara domin mu muna yi ne don kare martabobin kasashen mu sabanin abokan gaba wato boko haram da basu san zafirin abinda suke yi ba.
Wakilin muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5