Ina alfahari da sana’ar da nake yi yanzu tunda na daukewa iyaye na wasu daga cikin dawainiyar da ta rataya a wuyansu, domin a yanzu haka na fara karatuna na digiri na biyu, kuma da kai na na biya kudaden makaranta ta wannan sana’a tawa, a cewar Malama Sadiya Aliyu.
Sadiya Aliyu, 'Dagabana' wacce aka fi sani da Dagabes Beauty, matashiya mai sana’ar yi wa mata kwaliya, ta fara wannan sana’ar ne domin zama mai dogaro da kai, wanda a wancan lokaci tana sana’a ne ta hanyar wani ya fada wa wani sabani a yanzu.
Ta kara da cewa a yanzu da ta bude shago banda samun kwastamomi ta hanyar wasu wadanda ta yi wa a da, yanzu ko masu wucewa da zarar sun ga alamar shagonta ta na samu sabbin kwastamomi masu wucewa da suke zuwa wajenta.
Ko da yake Sadiya ta ce tana amfani da shafukan sadarwa wajen tallata kanta, sannan kuma bayan kwaliya ta kan sayar da kayayyakin turaren wuta, da su humra, baya ga dogayen riguna da ta ke sayar ma mata mussaman wadanda suka zo domin a yi musu kwaliya.
Har illa yau Sadiya ta ce babban burin ta shine ta bunkasa a harkokin da ta ke, duniya ta santa sannan ta zama sila da cusawa wasu matasa ra'ayin kasuwanci da zama masu dogaro da kai.
Your browser doesn’t support HTML5