Kamfanin Samsung, ya kaddamar da wata sabuwar waya mai suna “J2 Pro” wadda aka kirkireta don inganta rayuwar matasa da tsofaffi, musamman dalibai wadanda ke bukatar isashen lokaci don karatu, ba tare da wata hayaniyar duniya, ko yanar gizo ta daukar masu hankali ba.
Ita dai sabuwar wayar ta Samsung Galaxy J2 Pro, an inganata ta da duk wasu abubuwa da wayoyin zamani suke dauke da su, kamar su kyamara, damar aika sakon gaggawa da kira ko amsa waya.
Amma wayar bata da damar amfani da kafar yanar gizo ta G3, ko saukar da wasu manhajoji masu alaka da yanar gizo. Kamfanin dai yayi nazari wajen kirkirar wayar, don la’akari da irin yanayi da yara ‘yan makaranta ke bukatar lokaci don maida hankali a karatu.
Haka suma tsofaffin da basu da bukatar hayaniyar yanar gizo, za su ji dadin wayar don kuwa bata da duk wasu tsarin wayoyin zamani masu amfani da yanar gizo.
Baya ga damar amfani da yanar gizo, wayar na da duk wasu abubuwa da wayoyin zamani kanyi. An fara sayar da wannan sabuwar wayar ne a kasar Koriya ta kudu, akan kudi dalar Amurka dari da tamanin da biyar $185, kwatankwacin Naira dubu sittin da biyar.