Sabuwar Wayar Samsung Galaxy Note 9, Na Dauke Da Abubuwan Al-ajabi

Kamfanin Samsung ya bayyana wasu kadan daga cikin abubuwan da sabuwar wayar sa ta Galaxy Note 9, ta kunsa inda kamfanin ya bayyana cewar an inganta sabuwar wayar da batiri mai karko, haka kuma tana aiki cikin sauri kamar kyaftawa da bisimilla.

Wayar na dauke da wasu sababbin manhajoji da yasa ya zuwa yanzu wayar ta yi karanci a kasuwa, kuma wayar zata dan yi tsada wadda kudinta zai kai dalar Amurka $1,000 kwatankwacin naira dubu dari ukku da sittin.

Kamfanin dai ya maida hankali wajen kayata wayoyin sa a duk bayan shekaru, amma zai rika kyata tsarin da ya shafi na manhajoji a kowace shekara, amma inganta abubuwan da zai shafi jiki da yadda kalolin wayar zasu zo zai rika zuwa duk bayan shekara.

Sabuwar wayar nada karfin manhaja mai gyaran hoto wanda ake kira mai maida tsohuwa yarinya,manhajar zata gyara hoto da kanta ba tare da mutun ya wahalda kansa ba, tsarin ‘Automatic Photo Editing’ a turance.

A cewar Carolina Milanesi, mai kula da sashen kayatawa da zannen waya a kamfanin na Samsung, ta ce mutane ba zasu ga wani canji mai yawa ba musamman a bangaren da ya shafi yadda wayar ke aiki ‘Software’ amma suyin da wayar ke dauke da shi zai kara sa mutane su so wayar fiye da wasu wayoyin zamani.