Google ya fitar da wata sabuwar wayarsa ta Nexus 5X kasuwa a jiya Litinin, mai dauke da duk fasalolin zamani da ake bukata a wayar salula kuma mai saukin farashi.
Kamfanin LG ne ya kerawa Google wannan waya mai suna Nexus 5X, da yanzu haka aka fara sayar da ita kan shafunan yanar gizo, an dai fara sayar da wayar ne a kasashen da suka hada da Amurka da Birtaniya da Kanada da Ireland da Indiya da Koriya da kuma Japan.
Duk da yake wayar Nexus 5X bata da siffofi kamar sauran wayoyi irinsu Samsung da LG dama sauran kamfanonin dake kera wayoyin zamani, Google dai ya kirkiri wannan waya musammam ga mutane masu sha’awar manhajar Android, domin suyi amfani da ita ba tare da samun iyaka kan abinda zasu iya yi kan wayarsu.
“An kirkiri wannan waya ta Nexus ne domin samar da waya ta zamani mai dauke da fasahar zamani ba tare da kashe makurden kudade ba,” inji shugaban kamfanin LG a wata sanarwa da aka fitar.
Idan ba’a manta ba a watan Satumba ne kamfanin Google ya fitar da wayarsa ta 5X hade da wayar Nexus 6p wadda kamfanin Huawei yakera.