Hukumar binciken sararin samaniya ta NASA ta ce akwai yiwuwar samun ruwa mai kwaranya a duniyar Mars.
A wani bincike da masana kimiyya suka gudanar, sun kawo rahoto wanda zai iya zama babbar hujja cewa watakila akwai yiwuwar kananan rafuka da ruwa ke kwaranya a duniyar Mars, a kalla a lokacin zafi.
Shugaban sashen kimiyya na hukumar NASA, John Grunsfeld ya fada a wani taron manema labarai cewa wannan yana nuna yiwuwar samun abu mai rai a yanzu a duniyar Mars.
A shekara ta 2008, masana kimiyya sun bada tabbacin akwai daskararraren ruwa a Mars. Amma yanzu na’urorin dake dauke a kumbon binciken Mars na hukumar NASA sun yi nuni da mafi karkarfar hujja da aka taba samu na cewa narkakken ruwa mai kunshe da gishiri na malalaa wasu gangare na Mars kowanne lokacin zafi.
Daraktan ilimin kimiyyar duniyoyi na hukumar NASA, Jinn Green ya ce Mars ba duniya bace da take a kekashe a bushe kamar yadda muke zato a da. A wasu al’amura masu tabbatarwa an gano ruwa mai kwaranya a Mars.