Sabuwar manhajar nan ta masoya da kamfanin Facebook ya bada sanarwar fitowa da ita kwanan nan, zata taimaka wa masu amfani da shafin wajan ganowa da fallasa masu amfani da shafin wajan yaudarar mutane ta hanyar amfani da hotunan da ba nasu ba da kuma bayanan karya domin cimma wani buri nasu na daban, da kuma masu satar bayanan jama’a a yanar gido.
Kamfanin wanda ya fuskanci kalubale da dama akan rashin kare bayanan masu amfani da shafin sa lamarin da ya sa har majalisar dokokin Amurka ta gayyaci shugaban kamfani Mark Zuckerberg, domin amsa tambayoyin a majalisa.
Manhajar zata ba jama’a masu shekarun da suka kama da 18, damar bude shafi a manhajar wadda zata basu damar bayyana ra’ayin su akan irin mata ko mazan da suke so su nema ba tare da dukkan abokan da ke bin su sun gani ba.
Daga karshe wannan manhaja zata nuna inda mai shafin yake da kuma irin abokan da yake mu’amula da su da kuma kara dankon zumunci tsakanin jama’a a cewar jami’an kamfanin. Mun samo wannan labara ne daga mujallar Washington post, ta kasar Amurka.
Your browser doesn’t support HTML5