Sabuwar Manhajar Kayatar Da Abubuwan Sha'awa A Rayuwa

Wasu mutane da dama sun nazarci sabon tsarin manhajar gobe da nisa, “Augmented Reality” a turance. Wannan wani sabon tsari ne da za’a iya amfani da shi don kallo da tsara nau’in kwalliya da mutun zai yi sha’awar sakawa a daki ko gida.

Matasa a shekarar da ta gabata sun yi amfani da tsarin wasan TV-game, na “Pokemon Go” wanda yake samar da abokan wasa su bayyana a fili, wannan sabon tsarin zai wuce wanncan tsarin.

Sabon tsarin za’a iya amfani da shi wajen kwallon yadda za’a kayata daki a jikin na’urar da yadda idan an saka kaya wurin zai canza, a takaice zai saukaka wajen tsari da yadda mutane zasu samu sauki wajen kayatar da wuraren su.

Mutane zasu iya saukar da manhajar a wayoyin su, da zasu iya buga wasan game, da kallon tsarin ko hanyar kayatar da wuri gabanin siyan kaya da mutun zaiyi don tabbatar da cewar abun da mutun zai siya yayi dai-dai da abun da yake sha’awa.