Ana kyautata zaton sama da bayanan mutane miliyan guda masu anfani da shafin sada zumunta na facebook ne kamfanin sarrafa bayanai na burtaniya da ake kira Canbridge analytica ya yi amfani da bayanan su ba bisa ka’ida ba, yayin da ake kokarin gano yawan adadin mutanen da lamarin ya shafa daga miliyan 50 zuwa miliyan 87.
Shugaban katafaren kamfanin na facebook Mark Zuckerberg, da ke cigaba da fuskantar suka akan rashin kare bayanan miliyoyin mutane yaki daukar kwakkwaran mataki akan kamfanin na burtaniya, da kuma musanta maganganun da ake yi na cewa ya sauka daga mukamin sa na jagorancin kamfanin.
A wani taron manema labarai da ba kasafai aka cika ganin irin sa ba, shugaban kanfanin facebook Mr Zuckerberg, mai shekaru 33 da haihuwa ya kauce ma amsa tanbayar da aka yi masa akan kin amincewa ya halarta a gaban kwamitin bincike na majalisar Burtaniya.
Facebook Forum