Mata a duk fadin duniya na fuskantar kalubalen cin zarafi, ko dai a gidajen su, kasuwannin, makarantu da sauran wurare, hakan kuma na kara habaka a duk fadin duniya.
Duba da irin halin fargaba da mata ke shiga a duk lokacin da suka bar wurarren da suke da kwararan tsaro, hakan yasa wasu matasa a kasar India kirkiro wata na’ura da mata ko sauran mutane kan iya amfani da ita a duk lokacin da suka sami kawunansu cikin wani hali na bukatar taimakon daukin gaggawa.
Ita dai wannan na'ura za’a iya daurata a hannu kamar Agogo, kuma amfanin ta shine duk lokacin da mai daure da ita yake shakkar wani abu, sai kawai ya danna wani maballi a jikin nau’rar, yayinda ita kuma zata isar da sakon gaggawa ga iyalan mutun da jami’an tsaro mafi kusa.
Na’urar zata bayyana takamainmain wuri da mutun yake don kai agaji cikin sauri. Na'urar zata aika sakon gaggawa na text da na intanet, kana tana iya daukar magana na tsawon lokaci don amfani da shi idan bukatar hakan ta taso.
A cewar Manik Mehta, wanda ya kirkiri na’urar, da zarar mutane sun fahimci aikin wannan na’urar zasu ji shakkar yin wani abu ga duk wata mace mai daure da na’urar, za’a saki na‘urar a kasuwa wanda kudinta ba zai wuce kimanin dalar Amurka $40 ba wato dai-dai da Naira dubu goma sha biyar.