Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Ya Sake Toshe Wata Manhaja Mai Satar Bayanai


Katafaren kamfanin Apple, ya cire wata manhaja daga kasuwar manhajoji, da masu amfani da na’ura mai kwakwalwa Mac ke amfani da ita domin kariya daga masu kutse da satar bayanai a sakamakon zargin manhajar da aikawa wani kanfani dake kasar China bayanan binciken da mai amfani da na’urar yayi.

Wani mai bincike a fannin tsaro da kariyar bayanai a yanar gizo ne ya gano yadda manhajar da wani kamfanin yanar gizo mai suna Trend Micro ya inganta a kwana kwanan nan ke nadar bayanan binciken da mai na’urar yayi tana aikawa kanfanin.

Koda shike kanfanin ya musanta zargin cewa wannan mahaja na satar bayanan jama’a kuma tana aikawa kasar China.

Daga karshe kamfanin Apple ya jaddada cewa bayan cire manhajar da yayi daga kasuwar manhajoji, hatta aikin da zata iya gudanarwa a na’ura mai kwakwalya, ya dakatar da shi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG