Hajiya Halimatul Sadiya wacce aka fi sani da Sabuwa a shirin fim na Dadin kowa sabon salo, ta ce ta fara harkar fim shekaru 20 da suka gabata kuma tana shirin Dadin kowa ne domin fadakarwa da ilmantar ga alu’umma dangane da kalubalen rayuwa a yanzu.
Ta ce ta fito a matsayin Sabuwa matar Malam Ayuba mai gadi, mace mai hakuri da kuma yarda da kaddara, wacce take tarbiyartar da dan ta Dan asabe kan tafarkin da ya dace, da bashi tarbiya wajen bin biyayya da rashin raina sana’a.
Ta kara da cewa wannan fage da suke fitowa na nuni ne da yadda rayuwa ke wakana a gaske, da yadda mutane zasu yi da zarar sun tsinci kansu a wannan fage.
Daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta a shirin Dadin kowa ta ce baya wuce fita sassafe da suke yi domin gudanar da aikinsu, sannan da zarar ta fita mutane su kan yi tururwa domin su ganta duk da cewar ta na jin dadin haka kuma ta gamsu da cewar suna tasiri a cikin al’umma.
Ta ce lokacin da ta fara fim sai da iyayenta suka sanya hannu a takarda kafin a amince mata ta fara fim din, sannan wata damace na bada gudunmawar ga alummarta.
Ta ce fim din da dana yanzu akwai banbamci, duba da yadda ake shirya fim a da a wasu bangaren an cigaba wasu kuma yana bukata a inganta shi a ta bakin Sabuwa na shirin Sabon Salo.
Your browser doesn’t support HTML5