Daga dukan alamu batun canjin fasalin Kudi a Najeriya na cigaba da tada kura, domin duk da amincewa da tsarin da yawancin yan Majalisar kasa suka yi, Majalisar Dattawan Najeriya ta yi suka da kakkausar murya inda ta bukaci Babban Bankin Najeriya ya gaggauta tsawaita lokacin sauya tsofaffin kudi daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Yuni na shekara 2023.To saidai manazarta na ganin wannan karin ma ba zai isa a gama sauya kudaden ba.
Idan ba a manta ba, a ranar 26 ga watan Oktoba ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bada sanarwar sauya fasalin manyan takardun kudaden Kasar da Naira 1000 da Naira 500 da kuma Naira 200 a bisa hujjoji na maido da kudi Naira triliyan 2.7 daga cikin Naira triliyan 3.3 da ke hannun mutane zuwa bankuna, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi amanna da tsarin, har ya kaddamar da sabbin kudin, har aka bada wa'adin kammala sauya tsofaffin kudi zuwa sabbi cikin kwanaki 45 kacal, daga ranar 15 ga watan Disamba zuwa 31 ga watan Janairu na sabon shekara da za a shiga.
Wannan wa'adi ne ya sa Sanata Mohammed Ali Ndume mika wa Majalisar dattawa Kudurin tsawaita lokaci, daga kwanaki 45 zuwa watanni 6 a bisa wasu dalilai da ya bayyana. Ndume ya bada misali cewa a Jiharsa ta Borno a kananan hukumomi 5 ne kadai ake da bankuna, hasali ma akasarin mutanen jihar ba su da asusu a bankunan, ko an samu masu asusunma, ba kowa ne ya iya amfani da wayar hannu wajen mu'amala da kudi ba. Ndume ya nuna bakin cikinsa kan yadda aka kayyade yawan kudin da mutum zai iya cirewa a banki amma ba a kayyade yawan kudi da mutum zai iya kaiwa banki domin ajiya ba. Ndume ya ce ya kamata a ayi la'akari da kiran tsawaita ranar a matsayin wani lamari mai matukar muhimmanci ga kasa, domin dakile wahalhalu da 'yan Najeriya ke ciki.
Shi kuwa kwararre a fannin tattalin arziki na kasa da kasa Shuaibu Idris Mikati yayi tsokaci cewa Babban Bankin Najeriya ya kamata ya ji koke koken mutane wajen karin lokacin, saboda an samu akasi wajen kai sabbin kudade bankuna, kuma gashi ba a buga sabbin kudin da yawa ba. Mikati ya kara jaddada bukatar a duba muhimmancin hujjojin da ya sa aka yi tsarin tun farko, tare da kira ga CBN da ya kara lokaci.
To saidai ga daya daga Cikin Manyan Yan Canj a Kasar, Umar Garkuwa ya nemi yan majalisa su sake nazari akan wannan lamarin. Garkuwa ya ce binciken da yayi na nuni da cewa wadannan sabbin kudin ba za su iya daukuwa a na'urar ATM ba, kuma yana kalubalantar yan Majalisa akan aikin su na sa ido a harkar gudanar da kasa domin a samar wa talaka sauki. Garkuwa ya ce mai yuwa in an yi karin lokaci CBN zai iya gyara al'amarin.
Babban Bankin Najeriya ya fitar da sanarwa cewa, zai dauki muhimman matakan wayar da kan jama'a a shiyyoyi 6 na kasar, musamman a yankuna karkara, kasuwanni da al'ummomin da ba a kai masu manufofin ba tun farko, tareda yin sassauci wajen aiwatar da manufofi don magance rashin kudi da kuma sa ido kan tasirinsa.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5