Facebook ya fitar da wani sabon tsari da zai rika ankarar da mutane a duk lokacin da masu kutse na gwamnati ke kokarin shiga shafinsu domin satar bayanan su.
Babban jami’i mai kula da harkokin tsaro na kamfanin Facebook Alex Stamos, yace domin kare bayanan mutane sama da Biliyan ‘daya a duniya, idan muka lura cewa ana kokarin kutse cikin shafin mutum ko anyi kutsen har an saci bayanai, to zamu aika sanarwar da zata shawarci mutum ya kunna sabon tsarin da ake kira Login Approvals, wadda ita kuma zata ke aikawa mutum da wasu lambobi domin amfani da su wajen shiga shafinsa.
Stamos yace samun sanarwar ba yana nufin cewar an yiwa kamfanin Facebook kutse bane, yana nufin cewar a kwai matsala ga na’urar da mutum yake amfani da ita wajen shiga shafinsa, ya kuma kamata a dauki matakan da suka kamata wajen kare na’urar.
Duk da yake dai Facebook bai fadi ta yadda yake gano ire-iren kutsen da wasu gwamnatoci ke daukar nauyinsu ba, amma Facebook na amfani da wannan tsarin sanarwar ne idan har yayi imanin cewar anyi wa mutane kutse.
A shekara ta 2013 ne akayi zargin kasar Amurka da yiwa wasu kamfanoni tara kutse don satar bayanan mutane, ciki kuwa har da Facebook. Itama Koriya ta Arewa an zargeta da kutse bayan da aka kai hari kan kamfanin fina finai na Sony Picture Entertaimen, wanda yayi sanadin kwararar bayanai ma’aikatanta har dubu 6 kan yanar gizo, dama bayanai kan sabbin fina finan da basu fito ba, da albashin shugabannin kamfanin. Amma Koriya ta karyata zargin.
Shima shugaban kasar China ya musunta cewa kasarsa na aikata kutse a ziyarar da ya kawowa Amurka ta kwana kwanan nan.