Sabon Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya

Tedros Adhanom Ghebreyesus

An zabi tsohon ministan lafiya na ‘kasar Ethiopia Tedros Adhanom Gheybreysus, a matsayin shugaban hukumar lafiya ta Duniya, WHO. Tedros ya lashe zaben ne a zagaye na biyu lokacin da aka kada kuri’ar jiya Talata. Inda ya kada abokan takararsa David Nabarro na ‘kasar Birtaniya da Dakta Sania Nishtar likatan zuciya na ‘kasar Pakistan.

Tsohon ministan lafiyan kasar Ehiopia Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya fadawa taron kungiyar cewa ya kwashe tsawon rayuwarsa domin inganta lafiya da rashin daidaito da kuma taimakawa mutane a duk inda suke domin su gudanar da rayuwa mai kyau.

Ya kuma lura da cewa duk da hukumar lafiya ta duniya bata taba samun shugaba daga nahiyar Afirka ba, kada a zabe shi don kawai ya fito daga nahiyar Afirka, ke nan a zabe shi bisa cancantar sa.

Ya ci gaba da cewa “Amma, akwai amfanin zabar shugaban da ya yi aiki a ‘daya daga cikin guraren da ke da matukar matsala a fannin lafiya, kuma ya gyara ta fannin. Yace zai yi kokarin kawo sabbin hanyoyin gyara da duniya bata taba ganin irinsu ba.