Kundun tsarin mulkin Amurka bai yadda shugaban kasa ya hada harkokin kasuwancinsa da gudanar da ayyukan gwamnati dole ne ya bar daya
WASHINGTON DC —
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump yace zai tsame hannunsa baki daya daga kasuwancinsa don gudun sabanin tsakanin kasuwancinsa da shugabancin Amurka idan aka rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.
Nan bada dadewa ba zai zama shugaban mafi arziki, Trump ya fada a sakwanninsa na Twitter a jiya Laraba yace zai janye kansa daga kasuwancinsa.
Babu dokar Amurka da ta hana Trump fidda hanayen jarin sa, amma dai yace yana ganin bai dace ba a matsayinsa na shugaban kasa, saboda za a iya samun son zuciya.
Yace aikin shugabancin yana da muhimmanci fiye da duka wani abu.