Trump ya dora akan shafinsa na Twitter a jiya Laraba yana cewa komai na tafiyar daidai. Yace suna aiwatar da shirye shiryensu bisa tsari na zabo manyan jami’ansa da wasu mukamai.
Yace shi kadai ne ya san mutanen da, a bisa tabbas, zasu samu mukamai a sabuwar gwamntin tashi.
Kalaman nasa sun biyo bayan rahotanni da kafofin yada labarai na Amurka suke bugawa cewar komitin nashi na cikin rikici sakamaokn sallamar wasu mashawartarsa a kan tsaro daga cikin komitin nashi na karban mulki.
Trump ya caccaki jaridar New York Times wacce yace duk da zamanta daya daga cikin manyan jaridun duniya, tana cikin fushi saboda ana mata kallon kamar ‘yan jaridanta sakarkaru ne ko wawaye saboda irin labaran da suka bada kan shi Trump din a lokacin yakin neman zabe.
Har ila yau Jaridar ta Times ta rawaito cewar har yanzu ma’aikataun harkokin waje da hedkwatar sojan Amurka ta Pentagon suna zaman jira bayani daga komitin Trump, fiye da mako guda bayan zaben da aka yi mishi.