Baya ga jam'iyyar PDP ko shugaba Jonathan da ke cewa ko a zabi jam'iyyara Kara nausawa gaba ko kuma in an kauce a maida hannun agogo baya, ita kuwa APC na cewa za ta kawo canji, salon kampe na tone- tone ya kunno Kai a wannan karon musamman in da PDP ke dauko bayanai da nunaJanar Buhari na da tsaurin ra'ayi.
Kazalika a Wanann karon ne jam'iyya mai mulki ta kawo batun takardun makarantar Janar Buhari da ba ta yi hakan ba a karo na uku da ya ke takarar, inda hukumar zabe ta bakin mataimakin Daraktan labaru Nick Dazan tamaida martani na nuna gamsuwa ga cewa Buhari na da takardun makaranta kuma ba ta da ikon sauya shi don haka wanda bai gamsu ba ka iya zuwa kotu.
Koma dai yaya,wannan karo a fili ya ke jam'iyyar PDP da ke mulki tun 1999 na fuskantar mafi karfin dunkulalliyar adawa da hakan ke neman canza kalmomin kampe din zuwa sukar dan takara.
Karfin PDP da APC ta hanyar jarin gudanarda kampe a wannan karon ya fito fili da kananan jamiyyu ke ganin hakan ke sa ma su son takarar nemanmaida Najeriya mai jam'iyya daya ko biyu
Yunusa Tanko na jam'iyyar NCP da marigayi Gani Fawehinmi ya kafa na cewa hakan na kawowa dimokradiyya tarnaki.
Zafin kampe a wannan karo yayin da boma-bomaike tashi a wassu sassa da kuma mayarda martani mai zafiya sanya marubuci Ado Ahmed Gidan Dabino yin hannun ka Mai Sanda ga 'yan takara da sauran jama'a da nuna tarzoma ba ta da riba.
Alamun karatowar zabeko ma zafafar lamurra da tsaro ya sanya ko ma nan Abuja jirage ma su saukar angulu na shawagi inda sojoji ke ci gaba da duba motoci a mashigun garin.
Your browser doesn’t support HTML5