Ziyarar na cikin cigaba da fafitikar da shugaban yake yi na ganin 'yan Najeriya sun sake zabarsa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
A daidai lokacin da shugaban ke shirin kai ziyara jihar Nejan jam'iyyar ta PDP ta koka da yadda tace ana tuge allunan tanlar 'yan takaranta da hotunansu da dai sauransu. Alhaji Hassan Saba kakakin jam'iyyar a jihar Neja yace hotunan 'yan takaransu ana bi ana yagasu ko a konasu ko kuma a watsa masu fenti. Yace ko 'yan jam'iyyar APC ne ke yi masu ko kuma wadanda suke fakewa da ita APC din suna yi masu barna.
To amma tuni jam'iyyar APC ta nesanta kanta daga zargin. Mr. Jonathan Batsa jami'in yada labarai na APC a jihar yace wadanda suke yiwa PDP karya su ne suke yiwa jam'iyyar barna. Wadanda PDP ta ki basu kujerun takara su ne suke cire hotunan 'yan PDP din.
Dangane da zuwan shugaba Jonathan kakakin jam'iyyar Alhaji Hassan Saba yayi hannunka mai sanda ne ga al'ummar jihar. Yace sun yi imani shugaban zai isa jihar lafiya kuma zai koma lafiya. Su a jihar Neja suna mutunta duk wani shugaba. Janathan kuma shugaba ne na Najeriya. Yau yana wata jam'iyya Allah kuma na iya ba wani daga wata jam'iyyar kuma zasu bishi.
Ita ma jam'iyyar APC ta ja hankalin mabiya goyon bayanta game da ziyarar shugaba Jonathan. Jonathan Batsa ya kira mutanensu yace babu zage-zage babu fada.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.