Sabon Fim "Hakki" Zai Fayyace Hakkin Ma'aikaci Da Na Kamfani

Kwamred Kabiru Ado Minjibir

A karon farko kungiyar kwadago reshen jihar Kano sun gudanar da wata hadaka na kaddamar da wani fim mai suna 'Hakki' don wayar da kan ma’aikata hanyoyin sanin 'yancin a wuraren ayyuka da dama, kamar yadda shugaban ya bayyana Kwamared Kabiru Ado Munjibir.

Shugaban kungiyar kwadagon ya bayyana cewa da dama suna samun korafe-korafe daga bangaren ma’aikata, na matsalolin ma’aikata da basu san 'yancin kansu ba, mussamma ma wadanda ake korar su daga waje aiki ba tare da an basu hakkokinsu yadda suka kamata ba.

Sunyi hadin gwiwa da kamfanin 'Iyan Tama Multimedia' domin kaddamar da wannan fim din, ya ce daga cikin matsalolin akwai muhimmanci kafa kungiyoyin ma’aikata, matsalolin tauye hakkin ma’aikatan da suka samu wata tawaya a yayin da suke ayyukansu, da ma makamantan hakan.

Kwamrade Abbas Ibrahim

Daga nan ne kuma DandalinVOA, ya karkata akalar shirin nasa, ya zanta da shima wani jigo a kungiyar ta kwadugo, kuma shugaban kugiyar 'yan jaridu na jihar Kano kwamared Abbas Ibrahim, wanda yake cewa a nan kusa kadan ne zasu kaddamar da wannan fim na 'Hakki’ inda yake cewa matsalolin kwadago ne ya sa suka yi wannan hadakar.

Ya bayyana cewa wannan fim din, zai taimaka wajen bayyana menene hakkin ma’aikaci, sannan manene hakkin kamfani, kana fim din wata hanya ce ta isar da sakonni.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabon Fim "Hakki" Zai Fayyace Hakkin Ma'aikaci Da Na Kamfani 6'10"