Shirin mai suna "juyin sarauta" da shahararren marubucin labarun Hausa Ado Ahmed Gidan Dabino, da Hajiya Balaraba Ramat su ka shirya shi, da amfani da kayan gargajiya zalla da karin harshen Hausa na Dauri.
Falalu A Dorayi, shine mai ba da umurni na siliman, ya ce sai da ta kai su ga gina fada irin ta asali don dacewa da shirin.
Wani abu da na lura da shi, shi ne yunkurin yin fassara marar kura-kurai zuwa turancin Ingilishi a shirin da ya saba da yadda wasu fina-finan Hausa ke saba ka’idar nahawun turanci. A cewar Ado Ahmed, sun nemo kwararru a harshen turanci domin yin fassarar.
Cikin manyan bakin da su ka kalli shirin har da shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa Hadiza Bala Usman, wadda ta ce shirin ya burge ta kwarai da gaske, domin ya nuna yadda zamantakewa take a cikin gidan sauratar gargajiya.
Siliman, wanda ya lashe Naira miliyan 28 da nuna hakuri da yarda da kaddara shi kan ba da sarauta, bai shiga kasuwa ba tukun, amma ya samu lambar yabo na zama cikin tsari mai ma’ana da kunsar tsoffin ‘yan wasan Hausa irin su Chiroki.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5