Sabon Daftarin Kundin Tsarin Mulkin Guinea Zai Takaita Wa'adin Shugaban Kasa

Shugaban mulkin sojin kasar Guinea Mamady Doumbouya

Hukumomin rikon kwarya na Guinea sun gabatar da daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai rage tare da kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa, da kuma yiwuwar ba wa shugaban mulkin sojan kasar Mamady Doumbouya damar shiga zaben shugaban kasa mai zuwa.

A shekara ta 2022, gwamnatin mulkin sojan da ta karbi mulki a juyin mulki a shekarar 2021 ta ba da shawarar gudanar da mulki karkashin gwamnatin rikon kwarya na tsawon shekaru biyu kafin gudanar da zabe, bayan tattaunawa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, amma ba ta nuna alamar yunkurin shirya zabe ba.

Sabon daftarin tsarin mulkin da ake sa ran za a kada kuri'ar raba gardama da ba a yanke hukunci kai ba, zai iya ba da dama ga kasar mai arzikin tama da karafa a yammacin Afirka ta koma kan tsarin mulkin damokaradiya.

Magoya bayan hamayya na Guinea dauke da kwalin da aka rubuta "Zaben Gaskiya - Alamar Zaman Lafiya" lokacin wani gangamin da 'yan hamayya suka yi a Conkary ranar 31 Maris 2012, su na neman da a yi zaben 'yan majalisar dokoki na gaskiya a kasar.

Sabon shirin da aka gabatar a ranar Litinin a zauren Majalisar rikon kwarya ta kasa, wanda ke aiki a matsayin Majalisar dokoki a karkashin mulkin wucin gadi, bai hana mambobin gwamnatin da ke mulki shiga harkokin zabe ba.

Tsohon Shugaban kasar Alpha Conde, mai shekaru 86, wanda sojoji suka hambarar da shi kusan shekaru uku da suka wuce, ba zai shiga takarar ba saboda kayyade shekarunsa.

Alpha Conde

Alpha Conde yana gaida magoya bayansa lokacin yakin neman zabe. AFP.

Conde dai ya haifar da fushi da rashin kwanciyar hankali har zuwa juyin mulkin, bayan da ya sauya kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar sake tsayawa takara a karo na uku a shekara ta 2020, bayan hawansa mulki a shekara ta 2010.

Idan daftarin sabon kundin tsarin mulkin ya samu amincewa, za a zabi shugaban kasa na tsawon shekaru biyar wanda za a sabunta shi sau daya, wanda hakan zai rage wa'adin shugaban kasa daga shekaru shida a kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a shekarar 2020.

Ya zuwa yanzu dai ba a san lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasa ba.

Ku Duba Wannan Ma Shugaban MDD Ya Yi Kira Ga Sojojin Burkina Faso, Guinea, Mali Su Mika Mulki Ga Farar Hula