Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Dauke Da Makamai Sun Yi Awon Gaba Da Tsohon Shugaban Kasar Guinea Camara Daga Gidan Yari


Captain Moussa Dadis Camara
Captain Moussa Dadis Camara

Wasu mutane dauke da manyan makamai sun tafi da tsohon shugaban mulkin sojan kasar Guinea na shekarar 2008, Moussa Dadis Camara daga gidan yari a birnin Conakry da safiyar ranar Asabar tare da wasu manyan jami'ai uku a cewar Ministan Shari’ar kasar Charles Wright.

Mazauna yankin sun fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa motocin soja da na dakaru na musamman na sintiri a kan titunan babban birnin kasar Guinea, bayan da aka ji karar harbe harbe a gundumar Kaloum, inda aka tsare Camara da wasu a gidan yarin Central House.

"Da misalin karfe daya na safe agogon GMT wasu mutane dauke da manyan makamai suka kutsa cikin gidan yarin Central House da ke birnin Conakry. Sun tafi da mutane hudu da ake wa shari'a dangane da abubuwan da suka wakana a ranar 28 ga watan Satumban 2009, cikinsu har da Kyaftin Moussa Dadis Camara," a cewar Ministan Shari’ar kasar Charles Wright ta rediyo.

"Za a gano su a duk inda suke," a cewar shi, sai dai bai bayar da karin bayani kan binciken da suke gudanarwa.

Amma Wright ya ce an rufe iyakokin Guinea don hana su tserewa daga kasar.

Tun a shekarar da ta gabata ne dai Camara da wasu jami’ai ke fuskantar shari'a, bisa zarginsu da kitsa kisan kiyashi da fyade da jami'an tsaron kasar Guinea suka aikata a wani filin wasa, inda aka kashe mutane 150 a yayin wata zanga-zangar nuna goyon bayan dimokradiyya da aka yi a ranar 28 ga watan Satumban 2009.

Camara dai ya musanta cewa yana da hannu a aukuwar mummunan lamarin, inda ya dora alhakin kan wasu sojoji bata gari.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG