Wani sabon binciken jin ra’ayin mutane da aka yi ya nuna kusan Amurkawa shida cikin goma sun yi Imani da cewa cin hanci da rashawa a gwamnati ya ‘karu tun da aka zabi shugaban kasa Donald Trump, kuma yanzu fadar White House wuce Majalisar Amirka wajen cin hanci da rashawa.
Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Berlin Transparency International ta ce binciken da ta gudanar na jin ra’ayi ta yi amfani da Amurkawa dubu ‘daya a watan Oktoba da Nuwamba, wanda ya nuna kashi 44 cikin 100 sun yi imanin Trump da sauran jami’an fadar White House sun lalace wajen cin hanci da rashawa, an sami ‘karin kashi 36 daga irin wannan bincike da aka gudanar a shekarar 2016 shekarar karshe ta tsohon shugaban Amurka Barack Obama akan aiki.
Trump da fadar White House sun mayar da martani jiya Alhamis da cewa sun ‘dauki matakin kawo karshen cin hanci da rashawa da kuma ‘kara samar da gaskiya a gwamnati.
Kungiyar mai yaki da cin hanci da rashawa ta ce kusan mutane bakwai cikin 10 wadanda aka yi binciken akansu sun yi imanin gwamnatin Amurka ta gaza a yaki da cin hanci da rashawa, wanda ya ninka daga shekarar 2016. Kungiyar dai ta fassara cin hanci da rashawa a matsayin yin amfani da karfin iko wajen samarwa kai abin duniya.