Sabbin Matakan Tsaro Kan Fasinjoji da Jiragen Sama dake Shigowa Amurka Sun Fara Aiki Yau

Filin saukan jiragen sama

Sabbin matakan da Amurka ta fitar da zasu fara aiki yau akan duk fasinjoji da jiragen saman dake shigowa kasar kullum suna tattare da rudani.

Sabbin matakan tsaro akan duk wani jirgin sama da zai zo Amurka da zasu fara aiki a yau Alhamis, sun kawo rudani ga wasu kamfanonin jiragen sama.

“Sabbin matakan sun shafi duk wani mutum, matafiya na kasa da kasa, da Amurkawan dake komawa gida…. Daga filayen jiragen da jirgin zai tashi zuwa Amurka,” A cewar wata mai magana da yawun hukumar kula da tsaron ababane hawa, Lisa Farbstein.

Wannan dai na nufin dukkan fasinjoji 325,000 dake shiga Amurka a kullum zasu fuskanci karin matakan tantancewa.

Kamfanonin jiragen sama da dama sunce suna da hanyoyi iri daban-daban na yadda suke sarrafa fasinjojinsu a karkashin wannan sabon tsarin

Wasu kamfanonin irin su Emirate da EgyptAir da kuma Lufthansa sunce jami’ansu ne zasu yiwa fasinjojinsu tambayoyi.

Sauran kamfunna kuma kamar su Air France da Royal Jordanian, sunce zasu nema fasinjoji su rinka cike wata takarda mai dauke da tambayoyi.

Ana shawartar duk matafiya da su baiwa kansu karin isasshen lokaci idan zasuyi tafiya, ganin cewa zasu iya fuskantar a bata musu lokaci wajen tantancewar.