Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) yayi maraba da kasashe shidda sabbin mambobin kwamitin wadanda bana dindindin ba. Sabbabin shigar sune kasashen Equatorial Guinea da Ivory Coast da Kuwait da Netherland da Peru da kuma Poland.
Wadannan sabbin kasashen shida dai kasashe babban zauren MDD 193 ne suka zabe su don yin wa’adin shekaru biyu, wanda zai basu damar taka rawa wajen warware batutuwan samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
An daga tutocin sabbin kasashen shida a wajen ofishin kwamitin jiya Talata yayin wani bikin da aka shirya don yi musu marhabin.
Kwamitin Sulhu na MDD dai ya na da kasashe 15 a kansa, biyar daga cikinsu - watau China da Faransa da Rasha da Birtaniya da kuma Amurka – duk suna da wakilcin dindindin, kuma suna da ikon hawa kujerar naki kan duk wani abu da basu amince da shi ba.